Samun kudi a yanar gizo yana daya daga cikin hanya mafi sauki a wannan zamani domin zamani ne wanda dukkan kusan abubuwa ana yinsu ne ta hanyar amfani da yanar gizo. Yanar gizo ta bada damarmaki masu sauki da zasu taimakawa mutum ya mallaki dukkan kudin da ya keso ya mallaka. A wannan rubutun zamu duba wasu hanyoyi guda biya 5 wadanda zasu taimaka kawa mutum ya samu maqudan kudade a duk daga inda yake ta hanyar amfani da yanar gizo.
- Samun kudi ta hanyar Bayyana Ra’ayi (survey)
Samun kudin ta hanyar bayyana ra’ayi a yanar gizo na daya daga cikin hanyoyi mafi saukin samun kudin a wannan zamanin. A wannan zamanin da muke ciki kamfanunuwa kullum bibbiya sukeyi domin suji ra’ayi ko kuma irin magannganun da masu sayen kayansu ko kuma hajarsu suke fada akansu domin inganta kusuwanci da mu’amalar su da abokan huldarsu ta kasuwanci. Saboda haka kamfanunuwa suna biyan maqudan kudade domin suji ra’ayoyin mutane dangane da mu’amalarsu da abokan kasuwancinsu da kuma ingancin kayan da suke siyarwa a kasuwanni. Akwai kafafe ko kuma manhajoji da dama dasuke taimakawa mutane suje su bayyana ra’ayoyinsu akan wani abu su kuma a biyasu.
- Samun Kudi ta hanyar dora Hoto a Yanar Gizo
Sana’ar Daukar hoto yana daya daga cikin san’a mafi shura sannan mafin saukin samun kudi a wannan zamanin, daukar hoto da kuma dora shi a yanar gizo yana daya daga cikin hanya mafi saukin samun a yanar gizo. A wannan fagen abun da ake so shine mutum ya zabi abun da yakeso ya yake daukan hoto akansa a kawai manhajoji wanda zaka dora wannan hotunan akai kana sayarwa kana samun kudinka cikn kwanciya hankali.
- Qirqirar bidiyo ko kuma hoto mai motsi.
Daya daga cikin hanyoyi mafi shahara kuma mafi saukin samun maqudan kudade a wannan zamani shine qirqirar bidiyo. Idan mutum yana da wani ilimi ko kuma wata basira wacce mutane zasu iya koya su amfana, yin amfani da salon vedio wajen koyar da wannan ilimi ko kuma wannan san’ar na daya da ga cikin hayar da yakamata mutum ya runguma domin samun maqudan kudade a cikin sauki. Akwani manhajoji kala kala irinsu Youtube, TikTok, Instagram da sauransu wanda suke taimakawa mutum ya dora wannan bidiyon a kyauta kuma ya samu kudi dashi. A wannan bangaren ana buqatar jajircewa, mayar da hankali domin yin bidiyon zai ja hankalin masu kallo.
- Rubuce Rubuce a yanar gizo (Blog)
Tsarin blogging har yanzu yana cikin hanyayoyin samun kudin mafi sauki a yanar gizo, wannan wani tsari ne da zai taimaka maka ka mallaki wata manhaja ko kuma wani fage da zaka ke rubuce rubuce akan wani abu ko wani bangare da ya shafi ilimintarwa, bayar da labari ko kuma nishadantarwa. A nan ana buqatar mutum ya mallaki faji ko kuma manhaja (blog web) wacce zai ke dora waddannan rubuce rubucen akai wanda zai jawo mutane suke ziyartar wannan fagen nashi (blog web) domin samin karuwar ilimi ko labarai da dai shauransu. Yawan masu ziyartar da ake samu zai sa kamfanin Google su fara biyan mutum ta hanyar da ake cewa google adsent sannan akwai hanyoyi kala kala da mutum zai samu kudi dasu ta wannan tsarin kamar irinsu hada alaqa da wasu kamfanunuwa suna biyan ta hanyar tallata musu kayansu saboda yawan masu ziyartar fejin da dai sauransu. Wannan tsarin yana buqatar mayar da hankali da jajircewa domin yin rubutun da zaija hankalin mutane.
- Samun kudin ta hanyar yin shura a kafafen sada zumunta (Personal Branding)
Kafafen sada zumunta a wannan zamani sunzama wasu abubuwa na wajibi ko kuma wani bangare na jikin mutane domin sunzama wasu hanyoyin koyo da koyarwa, samun labarai, tallata kadara da dai sauransu. A wannan zamanin mutane sunayin amfani da kafafe sada zumunta domin ilimatuwa ko kuma nishadantuwa, wannan yasa zama shahararrer a kafafen sadarwa na zamani na daya daga cikin hanyar da zata sa mutum ya samu kudi sosai a kafafen sada zumunta. Idan mutum ya mallaki mabiya masu tarin yawa zai taimaka masa waje samun karbuwa a duk lokacin da yazo da wani abu domin ya siyar. Mutum zai iya samun kudi ta hanyoyi da dama a wannan tasrin kaman irin tallata kayan wani kamfani da dai shuran wasu hanyoyi.
A KARSHE
Samun kudi a yanar gizo abune mai sauki amma yana buqatar jajircewa, mayar da hankali da kuma wajabtawa kai neman ilimi. Duk hanyar da mutum ya zaba daga cikin hanyoyin da mukakayi bayani zai sami dukkan irin kudin da yake so ya mallaka. Yana da kyau ka fara tundaga yanzu domin sai anfara ake samun kwarewa.
0 Comments